News
China ta gargadi Amurka da Australiya kan barazanar tsaronta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kasar China ta yi kira ga kasashen Amurka da Australiya da su yi duk mai yiyuwa wajen wanzar da zaman lafiyar yankin gabashin duniya.
Kiran na zuwa ne bayan da rahotonni suka ce Amurka na shirin girke jiragen yaki shida masu harba muggan makamai a yankin arewacin kasar Australiya
Turkiyya Za Ta Bai Wa Najeriya Jiragen Yaki Marasa Matuka
Kafar yada labaran Autraliya ta ABC ta ce za a tsugunar da jiragen a sansanin sojin sama na Tindall da ke arewacin Australiya.
Ministan tsaron Australiya Matt Keogh, ya shaida wa manema labarai cewa ba ya tunanin samar da jiragen yakin Amurka a kasar zai iya kawo sabani tsakanin kasarsa da China.
Kawo yanzu dai Amurka ba ta ce komai ba game da lamarin.
Samar da jiragen yakin masu harba makaman da za su ci dogon zango na akalla kilomita 14, zai kara wa Amurka karfi, a yayin da ake ci gaba da fargabar cewa China za ta yi amfani da karfin soji wajen kwace iko da Taiwan.
