News
El-Rufa’i ya yi amai ya lashe kan biyan kudin makaranta
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce tsarin biyan kudin makaranta ga daliban sakandiren jihar da ma’aikatar ilimin jihar ta bullo da shi ya ci karo da tsare-tsaren gwamnatin jihar.
A baya dai ma’aikatar ilimin jihar ta fitar da sanarwar da ke cewa daliban sakandire a jihar za su fara biyan kudin makaranta
Chelsea ta dage kan Endrick, Utd na son Diaz, Depay zai tafi, Klopp na nadama
A wata sanarwa da mataimakin gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu gwamnan ya bayyana tsarin ilimi kyauta a matsayin babban burin da gwamnatinsa ta sanya a gaba.
Sanarwar ta ce gwamatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da tsarin ilimi kyauta ga daliban sakandire a fadin jihar.
