News
Gobara ta kashe mutane 3 a jahar Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku, biyo bayan wata gobara da ta tashi a kasuwar Badume da ke karamar hukumar Bichi a ranar Juma’a.
Ɗalibin BUK ya zama shugaban ƙungiyar LAWSAN ta Najeriya
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta cinye shaguna na wucin gadi 100.
“Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara na Bichi da misalin karfe 03:30 na safe daga wani Ibrahim Tsalha cewa gobara ta tashi a kasuwar kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 03:35 na safe. domin hana wutar yaduwa zuwa wasu shaguna.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
