Connect with us

News

2023: Za Mu Ci Zaben Gwamna Da Tsiya Ko Da Tsiya-Tsiya – Shugaban APC Kano

Published

on

Abdullahi Abbas shugaban APC ta kano

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin lashe zaben gwamnan jihar da za a yi a shekara mai zuwa da tsiya ko da tsiya-tsiya.

Advertisement

Da yake jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar da aka gudanar a karamar hukumar Gaya.

Amfani biyar game da samun man fetur a Arewacin Najeriya

Abbas ya bayyana cewa APC, kasancewar jam’iyyar da ke jagorantar jihar, ba za a iya kayar da ita ba.

Advertisement

“Mutane na cewa in daina cewa APC za ta kwace Kano da tsiya ko da tsiya-tsiya. Ina so in gaya wa wannan taron cewa APC za ta kama Kano da tsiya ko da tsiya-tsiya.

“A yau mun nuna kudurinmu na ganin mun ci zabe tun daga sama har kasa a shekarar 2023.Mun yi dukkan shirye-shiryen da suka dace, biki mai kayatarwa inda dan takarar gwamnan mu zai karbi tutarsa ​​daga hannun shugaban kasa da zai zo Kano domin ya ba shi tuta,” inji shi.

Advertisement

Ya kara da cewa karbuwa da daukakar jam’iyyar APC a jihar Kano ba a taba shakkun jam’iyyar ba, kuma jam’iyyar na tattare da maza da mata masu hikima wadanda za su iya ba da mamaki idan ana maganar cin zabe, yana mai jaddada cewa ta cika aikinta a cikin shekaru takwas da suka wuce.

Da yake magana a wajen, dan takarar gwamnan, wanda kuma shi ne mataimakin gwamna, Dakta Nasiru Yusif Gawuna, ya ce ya shirya tsaf domin tunkarar yakin da ke gabansa, ya san cewa yana da cikakken goyon bayan Gwamna Abdullahi Ganduje da duk masu fatan alkhairi na jam’iyyar.

Advertisement

Ina da tabbaci cewa kaddarata tana hannun Allah kuma ba ni da wata shakka ga Allah babu abin da zai hana ni cin nasarar zaben. Har yanzu jam’iyyarmu tana nan tana da karfin gaske kuma a shirye muke mu tsaya tsayin daka wajen fuskantar duk wata matsala,” in ji shi.Jaridar Daily Post ta rawaito cewa Ya yabawa magoya bayan jam’iyyar da suka halarci bukin fitar da tutar jam’iyyar da suka nuna kyakykyawan jin dadinsu da jajircewarsu wajen nuna wa kowa cewa a shirye suke don fuskantar kalubalen da ke gabansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending