Connect with us

News

’Yan Bindiga Sun Sace Wasu Mata A Kantin Magani

Published

on

Advertisements
ads

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

’Yan bindiga sun sace wasu mata biyu a wani kantin magani ranar Talata a Fatakwal, Jihar Ribas.

 

Advertisement

Majiyarmu ta ce, matan da aka sace sun hada da wata ma’aikaciyar kantin maganin da wata wata da ta kai danta shagon don a duba shi sakamakon rashin lafiya.

ƘARFIN HALI: Ɗan haya ya kai karar mai gida sabo da ta ƙi sayar masa da gida da ya ke ciki

 

Wani ganau ya ce, “Da alama ’yan bindigar sun bi sawun matar da ta kai danta mara lafiya kantin ne.

 

“Saboda tana sauka daga mota, barayin suka fito suka damke ta tare da ma’aikaciyar kantin sannan suka kara gaba,” in ji shi.

 

Advertisement

 

Tuni dai aka sanar da ’yan sandan yankin abin da ya faru domin su yi aikinsu.

 

Garkuwa da mutane, wanda gwamnatin Najeriya at ayyana a matsayin laifin ta’addanci, na daga cikin manyan kalubalen da suka addabi kasar duk kuwa da kokarin gwamnati da jami’an tsaro wajen yakar matsalar.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending