Wata kuri’a da aka kada a kasashe sama da 150, ya gano mata sun fi maza samun kai cikin bakin ciki, da damuwa da saurin fusata.
A shekarar 2012 rahotanni sun bayyana maza da mata sun yi kunnen doki ta fannin saurin fusata da rana, amma shekaru 6 bayan nan, adadin ya karu da kashi 6.
Matan Cambodia su ke jan ragamar yawan masu fushi da rashin farin ciki da kashi 17, yayin da Indiya, da Pakistan, da Moroco suke da kashi 12.
