News
CBN ya Jandda kudirin sa na daina karbar tsoffafin kudi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ranar 31 ga watan Junairu, 2023 domin tabbatar da ingancin tsohuwar takardar kudi ta N200, N500 da N1,000.
Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan bayan taron kwamitin kula da harkokin kudi na bankin (MPC) Kamar yanda Channels ta rawaito
Bankin na CBN ya kuma daga darajar tsarin kudi (MPR), wanda ke auna yawan kudin ruwa zuwa kashi 17.5 cikin dari.
A cewarsa, garkuwa da mutane da karbar kudin fansa ya ragu tun bayan da aka sake fasalin takardun kudi guda uku.
Ya kuma ce lokacin da aka bayar na musanya tsofaffin takardun kudi na Naira da sababbi ya isa ‘yan Najeriya su rika zuwa bankunan kasuwanci su karbi sabbin takardun kudi.
A ranar 26 ga Oktoba, 2022 ne CBN ya bayyana shirinsa na sake fasalin takardun kudi guda uku. Daga nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022, yayin da babban bankin ya sanya ranar 31 ga watan Janairu domin tabbatar da ingancin tsoffin takardun.
Akwai damuwa daga ‘yan Najeriya da dama kan yadda ake tafiyar hawainiya da sabbin takardun kudi na Naira uku a daidai lokacin da wa’adin ranar 31 ga watan Janairun 2023 ke gabatowa amma babban bankin ya dage kan cewa ranar ta tsaya.
A kwanakin baya ne dai CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su dakatar da biyan sabbin takardun kudi ta kan layi sannan su loda na’urorinsu na Automated Teller Machines (ATMs) tare da canza sheka na naira domin bunkasa yaduwa.
Babban bankin ya kuma kaddamar da shirin musanya kudade a fadin kasar domin baiwa wadanda ke yankunan da ba su da banki damar musayar tsofaffin takardun su da sabbin takardun kudi kafin cikar wa’adin.
Sai dai Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa da kuma Kungiyar Gwamnonin Najeriya sun bukaci babban bankin Najeriya CBN da ya kara wa’adin don baiwa ‘yan Najeriya damar samun sabbin takardun kudi.
