Connect with us

News

Kotu Ta Daure Matashi Shekara 4 Kan Satar ‘Pampers’

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kotun Majistare mai zamanta a Ikeja, Jihar Legas, ta daure wani matashi shekara hudu da rabi a gidan yari kan zargin satar kunzugun yara (pampers) wanda a kiyasce kudinsu ya kai Naira miliyan 13.5.

 

Advertisement

Ana tuhumar matashin da aikata laifuka uku da suka hada da hadin baki da sata da hana zaman lafiya.

 

Advertisement

CBN ya Jandda kudirin sa na daina karbar tsoffafin kudi

Alkalin Kotun, Lateef Owolabi, ya ce, “A wannan yanayi akwai bukar aika da sako mai karfi musamman ga mai kare kansa da ma al’umma.”

 

Advertisement

Ya fara ne da yanke wa matashin hukuncin zaman kurkuku na shekara guda ko biyan tarar N200,000 kan laifin hadin baki.

 

Advertisement

 

Sannan shekara uku a gidan yari ko biyan tarar N200,000 kan laifin sata, sai kuma wata shida a kurkuku ko biyan tarar N10,000 kan laifin hana zaman lafiya.

Advertisement

 

Kotu ta kuma bukaci mai kare kansa da ya maida kayan da ya sata din ga mai shi, Okuoromi Ehighamhe.

Advertisement

 

Owolabi ya ce yayin shari’ar, da fari mai laifin ya ki amsa tuhuma amma daga bisani ya amsa aikata laifin tare da rokon sassauci daga kotu.

Advertisement

 

Aminiya ta rawaito cewa Mai gabatar da kara, SP Josephine Ikhayere, ta fada wa kotun cewa a Agustan 2022 mai laifin ya hada baki da wasu wajen sace kaya, wanda hakan ya saba wa sassa na 411 da 173 da na 287 na Dokokin Haramta Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending