News
Najeriya Ta Yi Rashin Osinbajo A Matsayin Shugaban Kasa, in ji Sanusi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon Sarkin Kano, kuma shugaban Dariqar Tijjaniya na Nigeria Muhammad Sanusi II, ya ce Najeriya ta yi rashi saboda rashin samun mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban kasar.
Sanusi ya bayyana haka ne a wani taron kaddamar da littafi mai suna, “Osinbajo Strides: Defining Moments of a Innovative Leader,” a ranar Litinin.
Mataimakin ya kasance daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, wanda wasu suka caccaki tsohon ubangidansa kuma zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Sanusi, wanda kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN ne, ya lura cewa Osinbajo na daya daga cikin wadanda ke cikin wannan gwamnati da ke shirin tattaunawa kan al’amuran ci gaba.
Ya ce, “Kuma na ce, duk mun yarda cewa Nijeriya ta fi muni saboda rashin samun wani irinsa (Osinbajo) a matsayin shugaban kasa, amma ina fatan ya samu damar yin hidima da ba da shawara da kuma yin iya bakin kokarinsa a kasar kuma a ci gaba da yin aikj.
“Saboda haka, na tabbata a kowane irin matsayi ya samu kansa a nan gaba, kuma wata kila, za mu yi sa’a ya jagorance mu a wani lokaci ko kuma ya dauki wani matsayi na shugabanci a matsayin dan jiha.”
