Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta zama gwarzuwar gasar Serie A ta bana.
Karon farko cikin shekara 33, rabon da ta ci kofin tun lokacin Maradona yana kyaftin ɗinta.
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta tsaurara tsaro a gidan Messi da na Neymar saboda masu zanga-zanga
Nasrar na zuwa ne bayan canjaras da ta yi da Udinese a gidanta 1-1.
Ɗan wasan gabanta da ya fi haskakawa a wannan shekarar Victor Osimhen ya farke kwallon da aka fara jefa mata.
