Connect with us

News

An Ci Gaba Da Hako Mai A Borno Kwana 6 Kafin Saukar Buhari–NNPCL

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya ci gaba da aikin hako danyen mai a yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno, bayan shekara shida da dakatar da aikin.

Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kaddamar da dawowar aikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno, ta intanet a ranar Talata, kwana shida kafin saukarsa daga mulki.

Advertisement

Yanayin Shigar Rahama Sadau Zuwa Wajen Wani Taro Ya Bar Baya Da Kura

A shekarar 2017 ne aka dakatar da aikin neman danyen mai a rijiyoyin man masu suna Wadi-1 da kuma Kinasar-1, da ke yankin Tuba, sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai wa ma’aikatan da ke aikin a lokacin.

Sai dai daga bisani, bayan bincike da samun tabbacin tsaro, NNPC ta ci gaba da aikin a shekarar 2022 rijiyar mai ta Wadi-B

Advertisement

Babban Daraktan NNPCL mai kula da Hako Mai, Mukhtar Zanna, ya ce kamfanin ke amfani da fasahar zamani, kuma yana da kwarin gwiwar samun danyen mai da iskar gas da dangoginsu a rijiyar.

Shi ma a nasa bangaren, Aminu Maitama, wanda shi ne babban daraktan ayyukan hakar mai na NNPCL, ya ce, “Mun yi amannar cewa yawan danyen man da za a samu a yankin zai isa kasuwanci.”

Advertisement

Aikin dai ya fara samo asali ne daga shekarar 1976, da aka fara binciken gano danyen mai, a yankunan Gubio da Maiduguri da kuma Baga, kafin a ci gaba da shi a 1996.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending