Connect with us

News

Firaminitan Indiya, ya nuna gamsuwarsa, kan alaƙar ƙasarsa da Amurka.

Published

on

Narendra Modi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Firaminitan Indiya, Narendra Modi ya nuna gamsuwarsa, kan alaƙar ƙasarsa da Amurka.

Mista Modi ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya gabatar wa haɗakar zaurukan majalisun ƙasar a birnin Washington DC.

Advertisement

Ko a jikina kan maganar ci gaba da binciken bidiyon dala – Ganduje

Ya ce a yanzu ƙasashen biyu na son kyautata alaƙar haɗin gwiwa tsakaninsu.

Jami’an gwamnatin Amurkan sun yi ta yi masa tafi da jinjina yayin gabatar da jawabin, wani abu da ba a saba gani ba yayin da aka karɓi baƙuncin wani babban baƙo.

Advertisement

Shugaban na Indiyan, ya ce a yanzu zamanin zaman doya da manja tsakanin ƙasashen biyu ya zama tarihi, wani abu da ake kallo tamkar koma-baya ne ga ƙasar China.

Da yawa daga cikin mambobin jam’iyyar Democrat sun ƙaurace wa jawabin nasa, don nuna damuwa kan take hakƙin ɗan adam da suke zargin ana samu ƙarƙashin mulkinsa a Indiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending