Connect with us

News

Firaministan Holand ya yi murabus

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Firaninstan Holand Mark Rutte ya mika takardar murabus daga mukaminsa sakamakon sabanin ra’ayi kan siyasar kasar a game da bakin haure masu neman mafaka.

Advertisement

Murabus din ya biyo bayan jayayyar da aka share watanni ana yi tsakaninsa da kawancen jam’iyyun guda hudu da su kafa gwamnatin hadakaka da su a game da sabuwar turba da ake son dora kasar a kai.

‘Yan sanda na bincike kan matar da ta kashe mijinta a jahar Bauchi

A yayin taron manema labarai da ya yi jim kadan bayan murabus din, Mark Rutte ya bayyana yadda manufofinsa da na abokan tafiyarsa suka yi hannun riga, sai dai kuma ya nuna shawarsa ta sake tsayawa takara a nan gaba.

Advertisement

Tuni ma dai hukumar zaben Holand ta bayyana cewar za a shirya zaben ‘yan majalisar dokoki cikin tsukin lokaci wato a watan Nuwamba mai zuwa domin samar da sabon jagora wa  kasar.

Mark Rutte dai ya fara jan ragamar Holand a shekarar 2010, sannan kuma shine Firaminista wanda ya fi dadewa a kan wannan mukami a tarihin kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending