Connect with us

News

Mutane 6 sun mutu bayan  shan barasar da  abokinsu ya hada musu 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

An ce mutane 6 ne suka mutu bayan shan giyar gida da ake zargin wani abokinsu a unguwar Ogbogbo da ke karamar hukumar Ijebu-Arewa maso Gabas ta jihar Ogun.

An tattaro cewa  lamarin, ya faru ne a ranar Talata, a wani hadin gwiwa da abokai bakwai suka taru domin yin murna.

Advertisement

Buhari ya halarci ɗaurin auren ɗan gwamna Zulum a Borno

Rahotanni na nuni da cewa duk mutane shidan da suka sha barasa sun mutu, sai dai wanda ya kawo ruwan a gidansa bai sha ba.

Mazauna yankin sun bayyana cewa mutane shidan da suka mutu da wanda ake zargin sun samu sabani a baya, inda daga bisani aka sasanta.

Advertisement

Domin sasantawa da abokan nasa, an ruwaito wanda ake zargin ya bayar da kyautar gin na gida, inda aka ce ya je gida ya dauko.

DAILY POST ta rawaito cewa sa’o’i kadan bayan sun tafi da abokanan sun tafi inda suka nufa, labari ya nuna cewa biyu daga cikin abokan sun mutu yayin da wasu hudu ke kwance a asibiti.

Advertisement

Majiyar ta kara da cewa “sauran mutane hudu sun mutu washegari. An tabbatar da mutuwar mutane shida. Har yanzu ba a san inda mutumin da ya kawo barasa yake ba.”

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending