Connect with us

News

Gwamnatin Jahar Kano Ta Musanta Rahoton Mutuwar Mutum 10 A Rana Daya A Wani Asibitin Jihar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya musanta rahoton da aka wallafa a kafafen sada zumunta cewa marasa lafiya 10 sun mutu a rana daya a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase dake Nassarawa.

An rawaito wani Husaini Ahmad ya yi zargin cewa majinyata 10 ne suka mutu a wannan rana a asibitin, inda ya danganta mutuwar da sakacin jami’an asibitin.

Advertisement

Gamayyar kungiyar hadin gwiwa a Bauchi ta bukaci a yi wa Kanawa adalci a Kotun Daukaka Kara

Sai dai wata sanarwar hadin gwiwa da hukumar da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano suka fitar, ta ce an gudanar da bincike ba tare da bata lokaci akan bayanan asibitin daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa 10 ga watan Oktoba kuma ba a gano matsalar da ake zargi bat a mutuwar mutane 10 a rana guda.

Sanarwar ta kara da cewa, asibitin ya gudanar da bita ta kwanaki 10 kan mace-macen a duk fadin asibitin, inda aka gano cewa majinyata 15 ne kawai suka mutu a cikin kwanakin kuma a ranaku daban-daban.

Advertisement

A wani labarin kuma Gamayyar kungiyar hadin gwiwa a Bauchi ta bukaci a yi wa Kanawa adalci a Kotun Daukaka Kara

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending