Connect with us

News

Gamayyar kungiyar hadin gwiwa a Bauchi ta bukaci a yi wa Kanawa adalci a Kotun Daukaka Kara

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Gamayyar kungiya Coalition for Democratic Right (CDR) ta bayyana rashin jin dadin ta kan abin da ya faru a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano a watan da ya gabata.

Gamayyar dai tana maida martani ne kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki a kan jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) wacce ta lashe zaben kamar yadda INEC ta bayyana.

Advertisement

jami’ar Chicago: Martanin Atiku Da Obi Kan Rahoton BBC Na Rashin Samun Hujjar Zargin Tinubu 

“Yana da muhimmanci a tunatar da duk masu ruwa da tsaki cewa Kano tana da matsayi mai karfi a fannin tattalin arzikin Arewacin Najeriya; duk wani nau’i na rikicin siyasa a karshe zai dagula duk jihohin arewa.”

“A matsayinmu na gamayyar kungiyoyin da ke inganta dimokuradiyya, mun yanke shawarar kara zage damtse wajen tabbatar da cewa an ba da damar al’ummar jihar Kano; in ba haka ba, sakamakon ba zai haifar da komai ba illa nadama,

Advertisement

saboda tabarbarewar jihar Kano kamar kowace jiha ce Arewa ke dogaro da ita, saboda tsarin wurin da take da shi, da yanayin kasuwanci.”

“Muna so mu bayyana a fili cewa mu ba ‘yan jam’iyyar NNPP ba ne, kuma mu ’yan jihar Kano ne, amma muna daukar nauyin al’umma ne mu ja kunnen duk masu ruwa da tsaki wajen kokarin haifar da rikici a Kano.

Advertisement

 Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, yayin da yake dauke da alluna kan zanga-zangar lumana a kabarin Tafawa Balewa, Daraktan Sadarwa na kungiyar Ibrahim Babayo, ya bayyana cewa, “Tsarin dimokuradiyya shi ne ginshikin al’ummarmu, kuma ya zama wajibi kuri’ar kowane dan kasa ta kasance.

“Duk wani zarge-zarge na rashin da’a ko rashin bin ka’ida yayin zabe, dole ne a yi bincike sosai kuma a magance shi ta hanyar tsarin shari’a na gaskiya da adalci.”

Advertisement

Ibrahim Babayo ya ci gaba da cewa “Koken zaben gwamnan jihar Kano zai samar da adalci tare da bin doka da oda, wanda ke da matukar muhimmanci ga dorewar dimokaradiyyar mu ta shekaru 24 da ta gabata.

“Muna kira ga masu ruwa da tsaki, da suka hada da bangaren shari’a, hukumar zabe, jam’iyyun siyasa, da sauran jama’a, da su nuna gaskiya da adalci da bin doka da oda wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending