News
An Tantance Alkalai 11 Domin Zama Sabbin Alkalan Kotun Kolin Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar koli kan harkokin shari’a ta kasa NJC ta bada shawarar anada alkalai 11 amatsayin Alkalan kotun koli.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na majalissar, Soji Oye ya fitar a ranar Laraba, ta ce an cimma matsayar ne a karshen zaman majalisar na 104.
Gwamatin Tarraya ta kashe kusan Naira biliyan 3 don tura jami’an gwamnati zuwa COP28 a Dubai
Kundin tsarin mulkin kasarnan ya tanadi alkalai 21 a kotun koli amma a halin yanzu kotun tana da alkalai 10 mafi karanci a tarihi.
Hukumar NJC ta tantance ‘yan takarar zama Alkalan kotun koli 22 da hukumar kula da harkokin shari’a ta tarayya ta tantance, kuma a ranar Laraba ta zabi sunayen mutum 11 da suka yi nasara a shafinta na yanar gizo.
Ana sa ran hukumar ta NJC za ta mika sunayen ga shugaban kasa domin amincewa da su kafin ranar Juma’a.
A Wani labarin kuma Gwamatin Tarraya ta kashe kusan Naira biliyan 3 don tura jami’an gwamnati zuwa COP28 a Dubai
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
