Connect with us

News

Yunwa da kishin ruwa na yi wa Falasdinawa 500,000 barazana

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Falasdinawa dubu 500 ke cikin barazanar yunwa da kishirwa a biranen da hare-haren Isra’ila ke kara karuwa, kamar yadda gwamnatin Gaza ta bayyana.

Gwamnatin ta Gaza ta ce jama’ar birnin na cikin bala’i sakamakon dagangan Isra’ila ke kai hare-hare kan ababen more rayuwa da ke da alaka da abinci da ruwa.

Advertisement

Liverpool ta koma ta dayan teburin Premier League

Trt Afirka ta ruwaito cewa Mai magana da yawun birnin, Hosni Muhanna ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Asabar cewa karancin man fetur yana kawo cikas wurin kwasar wadanda suka samu rauni da kuma jigilar gawawwaki.

A wani labarin kuma Liverpool ta koma ta dayan teburin Premier League

Advertisement

Isra’ila ta ci gaba da zafafa kai hare-hare a Gaza bayan Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda zai bayar da dama a tsagaita wuta a hare-haren da Isra’ila take kaiwa Gaza.

Hamas da hukumomin Falasdinu sun yi Allah wadai da wannan matakin na Amurka a daidai lokacin da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa mutum 17,487 suka mutu a Gaza, akasari mata da yara.

Advertisement

Haka kuma wani hari da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Khan Yunis ya kashe mutum shida, inda wasu biyar suka mutu a wani hari na daban a Rafah, kamar yadda ma’aikatar ta tabbatar a ranar Asabar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending