News
Majalissar Wakilan Najeriya Ta Bada Umarnin Gayyatar Tsohon Ministan Sufurin
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufurin jiragen sama da ya gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, domin ya yi mata bayanin halin da kamfanin jirgin sama na kasa, Nigeria Air, ke ciki, zuwa lokacin da ya bar mulki.
Ana saran tsohon ministan zai bada haske a kan batutuwa da dama da suka shafi aikin.
Wasanni suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban matasa – Gidauniyar Bukola Saraki
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Tarkighir Dickson ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis.
Da yake gabatar da kudirin, Dickson ya ce gwamnatin da ta shude ta kashe biliyoyin kudade domin samar da sabon kamfanin jirgi na kasa amma har yanzu ba a san matsayin aikin ba.
Idan dai za a iya tunawa a watan Satumba ne Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ya dakatar da aikin na Najeriya Air.
A wani labarin kuma Wasanni suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban matasa – Gidauniyar Bukola Saraki
Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da zaɓen da aka yi wa Peter Mbah na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Enugu a zaɓen gwamnan jihar na watan Maris.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a zaman da ta yi yau Juma’a.
A lokacin zaman nata, ɗaukacin alƙalai biyar na kotun sun yi watsi da ƙarar da jam’iyyar LP da ɗan takararta na gwamnan jihar, Chijioke Edeoga suka ɗaukaka suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.
Kotun ta bayyana cewa babu wata hujja ƙwaƙƙwara da aka gabatar wadda zai sanya ta ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da kuma na kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar ta Enugu, waɗanda dukkanin su suka tabbatar da nasarar ta Mbah.
Sakamakon zaɓen gwamnan na jihar Enugu da Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta fitar dai ya nuna cewa Peter Mbah shi ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 160,895.
