Connect with us

News

Gwamnan Ondo, Akeredolu ya rasu Yana da shekaru 67 a duniya.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Jaridar SaharaReporters a ranar Laraba cewa Akeredolu ya mutu a Legas.

SaharaReporters ta gano cewa likitocin fadar gwamnatin jihar ne ke kula da shi har zuwa rasuwarsa saboda ba za su iya kai shi kasar waje ba.

Yan Majalissar Dokokin Najeriya Na Shirin Katse Hutu Domin Amincewa Da Kasafin 2024

“Akeredolu ya mutu; ya rasu ne a Legas Yana da shekaru 67 a duniya.,” inji majiyar.

Gwamnan da ke fama da rashin lafiya ya dawo Najeriya a cikin watan Satumba bayan hutun jinya na watanni uku a kasar Jamus, kuma a kwanan baya ya ci gaba da wani taron bayan da shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya mika mulki ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.

Mataimakin sa, Aiyedatiwa ya tsaya a matsayin mukaddashin gwamna.

Advertisement

Bayan dawowarsa Najeriya a watan Satumba, Akeredolu ya zauna a Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda ya yi kokarin gudanar da mulkin jiharsa daga can, lamarin da ya janyo cece-ku-ce tsakanin jama’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending