News
Tallafin Naira miliyan 200 : Ba Gaskiya Ba ne, Har Yau Ko Mudun Shinkafa Ba A Raba Mana Ba – Sanatoci
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Majalisar Dattawa ta ƙaryata zargi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa, cewa sun karɓi kayan tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa zuwa mazaɓun su.
Hadimin Yaɗa Labarai na Shugaba Bola Tinubu, Olusegun Dada, shi ne ya fito a shafin sa na Tiwita, wato X a yanzu, ya wallafa cewa sanatoci sun karɓi kayan tallafi na Naira miliyan 200, su kuma mambobin Majalisar Tarayya sun karɓi kayan tallafi na Naira miliyan 100.
“Bayan jinkirin da aka samu, a yanzu dai zan iya tabbatar da cewa Sanatoci da Mambobin Tarayya sun fara jidar kayan tallafin da Gwamnatin Tarayya ya yi masu masu alƙawarin ba su, domin su je mazaɓun su, su raba kayan domin samar wa marasa galihu sassaucin raɗaɗin tsadar rayuwa. An raba kowane Ɗan Majalisa kayan abinci na Naira miliyan 100. Sanatoci kuma an raba wa kowane kayan abinci na Naira miliyan 200, domin su raba a yankunan su.” Inji hadimin shugaban ƙasa.
Premium Times ta ruwaito cewa Da su ke maida martani ta bakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula da Kafafen Yaɗa Labarai, Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa shi dai har yanzu ko mudun shinkafa da sunƙin taliya ba a kawo masa ba, ballantana kuma kayan masarufi na Naira miliyan 200 daga gwamnatin tarayya.
Adaramodu ya yi ƙarin haske cewa ya ɓebi kuɗin aljihun sa da kuma kayan abinci ya raba wa mazaɓun sa, domin sauƙaƙe wa jama’a yin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara. Ya ce ba gwamnatin tarayya ce ta ba shi kuɗaɗen da ya raba ba.
“Shin Minista ce ta ce ta raba mana kuɗin ko kuwa Shugaban Ƙasa? Saboda Ni dai idan ma an raba ɗin, to ni dai ba a ba ni ko sisi ba, kuma ko mudun shinkafa ɗaya ban gani da sunan tallafin shugaban ƙasa ba.”
“Ai da sun ba mu kayan abincin tallafin, to da an ga lodin tirelolin kayan abinci sun riƙa karakaina a faɗin yankunan mazaɓu na, a Jihar Ekiti, Ondo, Oyo da sauran jihohi. Kuma da yanzu an ga jama’ar yankunan mu cike da farin ciki idan suka samu wannan tallafi na gwamnatin tarayya.”
Ezrel Tabiowo, Jami’in Yaɗa Labaran tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce kwata-kwata bai san da labarin raba kayan tallafin ba. Ya ƙara da cewa duk abin da Sanata Lawan ya raba, da kuɗin aljihun sa ya yi hidimar, daga Gidauniyar sa ce.
“To shin Naira miliyan 200 nawa ta ke ne a wannan mawuyacin halin da ake ciki? Ko fa geron da za a raba a Shiyyar Sanata ɗaya ba za su isa ba, ballantana sauran kayan masarufi.
“Idan ka yi lissafi, Naira miliyan 200 za ta sayi buhun shinkafa 6000 ne fa kaɗai, idan ma aka ce Naira 30,000 za a sayi kowane buhu 1.” Cewar sa.
