Connect with us

News

‘Yan bindiga sun bukaci a biya diyyar naira miliyan 50 kan tsoho mai shekaru 70 da suka kama

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da wani tsoho mai shekara 70 Pa Adeife Adelaja sun bukaci a biya su naira miliyan 50 kafin su sake shi.

Masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da Pa Adelaja wanda yana daga cikin dattawan cocin RCCG dake Ijebu Igbo dake karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar Ogun kuma mai kiwon aladu ranar 31 ga Disemba yayin da yake hanyar zuwa coci da dare.

Advertisement

Kotu ta tura tsohon Ministan Makamashi kurkuku, bayan tartsatsin harƙallar wutar Mambilla 

Wani majiya kuma makusancin iyalinsa Adelaja ya ce diyyan da maharan ke bukata ya yi yawan da iyalinsa ba za su iya biya ba.

“Zuwa yanzu ana maharan su rage kudin da suka mabata a biya su.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abiodun Alamutu ya tabbatar cewa rundunar ta fara farautar maharan domin ceto tsohon da hukunta maharan

A wani labarin kuma Kotu ta tura tsohon Ministan Makamashi kurkuku, bayan tartsatsin harƙallar wutar Mambilla 

Advertisement

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Advertisement

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending