Connect with us

News

Mutum biyu sun mutu, 77 sun jikkata a fashewar da ta faru a Ibadan

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnan jihar Oyo, a kudancin Najeriya, Seyi Makinde ya tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu mutane 77 suka jikkata a wata fashewar da ta faru a ranar Talata da yamma.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da duka wadanda suka jikkata kuma suke samun kulawa a asibiti.

Gwamnatin jihar Kano ta ware biliyan 8 domin gina manyan makarantun firamare guda uku a fadin jihar.

Makinde ya kara da cewa kuma su samar da matsuganai na wucin- gadi ga mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon al’amarin.

Advertisement

Gwamnan wanda ya ziyarci inda lamarin ya faru a Bodija da ke Ibadan babban birnin jihar ya ce, bayanan farko daga jami’an tsaro sun bayyana abun da ya janyo fashewar.

Inda ya kara da cewa wasu masu aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne da ke zaune a wani gida a wurin suka ajiye abubuwa masu fashewa, kuma su ne suka haddasa fashewar.

Advertisement

Hotunan lamarin da ke yawo a dandalin sada zumunta sun nuna yadda fashewar ta shafi gidaje da motoci da kuma nisan wurin da fashewar ta shafa.

Hukumar kai agajin gaggawa ta NEMA tace an tura ma’aitakai kai dauki da jami’an tsaro, jami’an kashe gobara, jami’an hukumar civil defence da sauransu, domin ayyukan ceto a wurin da lamarin ya auku.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending