Connect with us

News

Nan Da Makonni Uku Ɗalibai Za Su Fara Karɓar Bashi Daga Gwamnatin Nijeriya

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu

 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu Zai Kaddamar Da Kwamitin Gyaran Mafi Karancin Albashi Ranar Talata

Advertisement

A wata sanarwa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila ya fitar a baya-bayan nan, ya bayyana cewa shirin bayar da lamuni ga dalibai na gwamnatin tarayya za a kaddamar da shirin nan da makonni biyu zuwa uku masu zuwa.

Ba Za Ta Iya Ci Gaba Da Biyan Tallafın Wutar Lantarki Ba – Gwamnatin Tarraya

Wannan tabbacin na zuwa ne a wata ganawa da wakilan kungiyar dalibai ta kasa (NANS) suka yi da shugaban ƙasa a fadarsa da ke Abuja.

Advertisement

Gbajabiamila ya ba da tabbacin cewa, an fara shirye-shiryen wanda ya yi nisa sosai don aiwatar da shirin.

Da yake jawabi game da matsalolin da ke tattare da shirin, Gbajabiamila, ya bukaci dalibai da su bayar da shawarwari wanda za su inganta shirin.

Advertisement

Gbajabiamila ya jaddada muhimmancin shirin a matsayin wani bangare na inganta manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma kudirinsa na bunkasa ilimi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending