Connect with us

News

Ba Za Ta Iya Ci Gaba Da Biyan Tallafın Wutar Lantarki Ba – Gwamnatin Tarraya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Ministan Wutar Lantarki na Nijeriya Adebayo Adelabu ya ce kasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafın wutar lantarki ba, yana mai cewa dole ne Nijeriya ta fara komawa kan tsarin kudin fito mai inganci, domin a halin yanzu kamfanonin da ke samar da wutar lantarki (GenCos) na bin kasar bashin Naira tiriliyan 1.3 da kuma kamfanonin iskar gas masu bin ta bashin dala biliyan 1.3.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka yi a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce Naira biliyan 450 ne kawai aka ware domin tallafin lantarki a bana amma ma’aikatarsa na bukatar sama da naira tiriliyan biyu domin biyan tallafın.

Advertisement

Hukumar FCTA Ta Rushe Gidaje Dubu 15 Da Aka Gina Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Unguwar Gwarinpa Da Ke Abuja

Tun a farkon wannan watan na Fabrairu ne aka rawaito ministan yana jaddada batun cewa ya kamata a cire tallafın lantarki a Nijeriyar, yana mai cewa a shekarar 2023 da ta gabata gwamnatin tarayya ta kashe naira biliyan 700 a biyan tallafın mai.

Batun da ministan ya yi a makon da ya wuce ya jawo mayar da martani daga mafi yawan yan kasar da ke nuna adawa da hakan.

Advertisement

Ko a ranar Litinin ma Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF ya bukaci Nijeriya ta cire tallafın lantarki da na man fetur baki daya, a matsayin wani bangare na matakan magance matsololin tattalin arziki da kasar ke fustanta.

IMF ta fadi hakan ne a wani rahoto da ta fitar bayan kammala nazari kan sha’anin kudi na Nijeriya. IMF ta ce hakan ya zama wajibi ne saboda tallafın baya isa ga wadanda ake son su amfana da shi.

Advertisement

Ya ce a yanzu za a bar gwamnatocin jihohi su rika samar da wutar lantarki ba tare da kashin kansu ba don samar da wutar lantarki ga jihohinsu.

Da yake magana a kan tashar da ta durkushe kusan sau shida tsakanin watan Disambar 2023 zuwa yanzu, ya ce hakan ya faru ne sakamakon karancin iskar gas da tsufa injina da karancin karfin wutar lantarki da aka samu, da lalata tashoshin wutar lantarki a wasu sassan kasar.

Advertisement

 Channels TV ta rawaito ministan a wajen taron yana karawa da cewa Kamfanin da ke isar da wutar ga yankuna a fadin kasar yana da ayyuka sama da 100 da aka yi watsi da su saboda bambancin alkaluman kwangilolin da ake samu a sakamakon tashin farashin kayayyaki, don haka kamfanin ba zai ba da wasau sabbin kwangiloli ba har sai an kammala duk irin wadannan ayyuka.

Ministan ya kuma ce an ware sama da Naira biliyan 50 a kasafın kudin shekarar 2024 domin gina kananan cibiyoyin samar da wutar lantarki ga lunguna da sako-sako na kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending