Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 3 Tare Da Yin Garkuwa Da Wasu 30 A Jihar Nejan

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

Wasu yanbindiga sun hallaka mutane 3 tare da yin garkuwa da kimanin mutanen 30 a jihar Neja

Advertisement

Bayanai daga Yankin Bassa ta karamar Hukumar Shiroro na nuna cewa da safiyar ranar Alhamis din nan maharan suka aukawa wannan yanki,

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansh ya shaidawa VOA Hausa cewa daga cikin mutane biyu da aka kashe jami’an tsaro ne na ‘yan banga, sannan yace daga ranar Lahadin da ta gabata zuwa yanzu, sama da mutane 13 maharan suka kashe tare da yin Garkuwa da kimanin Mutane 40 a wannan yankin.

Advertisement

Shugaban karamar hukumar Shiroron, Hon. Akilu Isyaku Kuta yace yankin na Shiroro ya na cikin tashin hankali domin kuwa yanzu haka, mayakan Boko Haram suna dasa bama-bamai a hanya.

Ya zuwa yanzu dai babu wani karin haske daga rundunar yansanda ta jihar Neja akan wannan sabon hari domin kuwa kokarin samun kakakin ‘yan sandan, Wasiu Abiodun yaci tura,

Advertisement

Amma Kwamishinan Kula da Harkokin Tsaron cikin Gida na jihar Neja Janaral Bello Abdullahi Muhammad mai ritaya ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace gwamnati na kokarin tabbatar da tsaro a wannan yanki.

Fatan Mutanen wannan yanki dai shine kara jibga jami’an tsaron sojoji a wannan yanki domin samun saukin wannan lamari.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending