Connect with us

News

Akwai fursunoni da dama da ake tsare dasu a gidan yarin Kurmawa, Kano haka kawai

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kwamitin ba gwamnati shawara kan matsalolin gidajen yari da yadda za a warware matsalolin wanda Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun ya kafa, ya ce ya gano fursunoni sama da 300 da ke jiran shari’a a kurkukun Kurmawa da ke Kano, ba tare da cikakkun bayanai na shari’arsu ba.

Kwamitin ya gano haka ne a lokacin da ya kai ziyarar bazata wannan gida inda ya gano cewa wasu na zaune ne kawai ba tare da takardun bayanan irin laifin da suka aikata ba.

Kashi 15 ne kawai ake tuhumarsu yayin da Kano ke samun rahotannin fyade sama da 1,000 duk shekara – NAWOJ

Kwamishinan ƴansandan Kano Muhammed Hussaini Gumel ne ya ke jagorantar wannan kwamiti.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ziyarar, Gumel ya ce aikinsu shi ne gano irin wadannan abubuwa sannan su rubuta su da kuma mika su ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace.

Da yake gabatar da wasu fursunonin da suka shafe shekaru suna jiran shari’a a gidan yarin Kurmawa, jami’in hukumar gidan yarin, ya bayyana cewa mafi yawansu ba su da wani ba su da cikakken takardun laifi koshari’a ko ma wani laifi kafin a daure su.

Advertisement

Ya ce da yawa daga cikin su ba shaidar aikata laifi da suka yi sannan wasu kuma ba a san me ma suka aikata ba ballantana a ki su kotu, kawai an jiye su shekaru da dama a gidan yarin suna jiran ikon Allah.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending