Connect with us

News

Majalisar wakila ta yi yunkurin  kara yawan tarar da ake ci kan wadanda aka samu da lefin wulakanta Tutar Najeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Majalisar wakila na wai yunkuri domin kara yawan tarar da ake ci kan wadanda aka samu da lefin wulakanta Tutar Najeriya daga naira 100 zuwa naira dubu 100.

A jiya ne kudirin yin gyara kan girmama Tutar Najeriya ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilan.

Akwai fursunoni da dama da ake tsare dasu a gidan yarin Kurmawa, Kano haka kawai

Dan majalisa Sada Soli na jam’iyyar APC daga jihar Katsina wanda ya gabatar da kudirin, ya ce ana samun daidaikun al’umma da kuma jama’ar gari da wasu kungiyoyin dake wulakanta tutar Najeriyar.

 

Da yake yanke hukunci kan kudirin, Mataimakin shugaban majalsiar Benjamin Kalu ya mika kudirin gaban kwamitin majalisar daya da ce domin daukar mataki na gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending