Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Alkawarin  Hadin Gwiwa Da Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta  The Association of Online Media Guild

Published

on

 

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Alkawarin  Hadin Gwiwa Da Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta  The Association of Online Media Guild

 

Kungiyar mawallafa jaridun yanar gizo ta  The Association of Online Media Guild ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya, wanda ya samu halartar ‘yan jaridu daga kungiyoyin yada labarai daban-daban a fadin jihar Kano.

A yayin bude taron, kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya yi jawabi ga mahalarta taron.

Da Ɗumi-Ɗumi-Ƴan Bindiga Sun Dira Wata Makaranta,Sun Yi Awon Gaba Da Ɗalibai A Kaduna

Ida ya taya  Kungiyar mawallafa jaridar yanar gizo ta  The Association of Online Media Guild, kuma muna ba ku tabbacin goyon bayanmu tare da idan akwai wuraren da za mu iya ba da tallafi, za mu yi hakan,” in ji Kwamishina Dantiye.

Advertisement

Ya jaddada mahimmancin yaki da labaran karya da ke da alaka da kafafen yada labarai na  yanar gizo tare da bayyana banbance-banbance tsakanin kwararrun ‘yan jaridu da sauran su.

Dantiye ya bukaci a rika bin ka’idojin aikin jarida tare da karfafa gwiwar ‘yan jarida da su yi amfani da fasaharsu wajan samar da sahihan bayanai.

Sunusi Bature Dawakin Tofa babban sakataren Yada labaran Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf Sunusi Bature , ya jaddada kyakkyawar alakar da ke tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai. Ya yabawa kungiyar bisa samar da wani dandali na bunkasa aikin jarida a Jihar Kano

“Muna daukar kafafen yada labarai na yanar gizo da muhimmanci a gidan gwamnatin Kano. Za mu sake duba batun  kafafen yada labarai na yanar gizo tare da Kungiyoyin Kafafan Yada Labarai ,” in ji Dawakin Tofa.

Shugaban kungiyar na rikon kwarya Abdullateef Abubakar Jos, ya bayyana kungiyar ‘yan jarida ta yanar gizo a matsayin kungiyar ‘yan jarida da ke aiki ta yanar gizo tare da mambobinta a fadin Najeriya, mai hedikwata a Kano. Ya jaddada kudurin inganta aikin jarida na da’a da kuma isar da sahihan labarai.

A karshen taron, mahalarta taron sun karbi takaddun shaida, wanda ke nuna nasarar kammala shirin  na kwana daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending