Connect with us

News

Dalilin da yasa na saka wuta a Masallaci – Wanda ake Tuhuma

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano, ta tabbatar da kama wanda ake zargi da saka wuta  a wani masallaci da sanyin safiyar yau a kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar.

Advertisement

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Usaini Gumel, ya shaidawa Kamfanin Dallancin Labarai na Ƙasa NAN a wata hira ta wayar tarho a ranar Laraba cewa an kama wani matashi mai shekaru 38 Shafi’u Abubakar kan lamarin.

1 Daga Cikin Mutanen Da Aka Cinna Wa Wuta A Masallaci A Kano Ya Rasu

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin kai hari masallacin ne saboda takaddamar da aka dade ana yi tsakanin dangi kan rabon gado.

Advertisement

“A ranar 15 ga watan Mayu, 2024, da misalin karfe 5:20 na safe ‘yan sanda sun samu rahoton fashewar wani abu a wani masallaci da ke kauyen Gadan a lokacin sallar asuba, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

“Nan da nan, an tura wata tawagar jami’an tsaro, ciki har da kwararru masana abubuwan fashewar sinadarai da Radiyo da kuma Nukiliya (EOD-CBRN), zuwa wurin.

Advertisement

“An garzaya da mutane ashirin da hudu da suka hada da maza 20 da yara hudu wadanda suka samu raunuka daban-daban zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano domin yi musu magani,” inji shi.

CP ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa fashewar bam ne ya tashi kuma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike.

Advertisement

Ya ce ‘yan sandan na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su fitar da karin bayani nan gaba kadan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending