News
Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa Ƙarƙashin Jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta lura da halin da Kano ke ciki domin ya shafi martabarmu sarauta a ƙasar Hausa.
Cikin wata sanarwa a rubuce da jaridar Daily Trust ta wallafa, majalisar ta yi kira ga dukkanin ɓangarorin biyu da su tabbatar da gudanuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma rahotanni sun bayyana cewa guda daga ciki ya garzaya kotu don haka yanzu magana na ƙarƙashin shari’a.
Masallata Sun Rasu Suna Tsaka Da Sallah A Yayin Da Masallaci Ya Rufta Musu
Sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin gudanarwa mai martaba Lawal Hassan Gummi OFR, Sarkin Gummi. Shugaban Kwamitin Gudanarwa na majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC).
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
