News
Tinubu ya aikewa majalisar kasar nan kudirin mafi Karancin albashi na naira 70k
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Shugaban Kada Bola Ahmad Tinubu ya bukaci majalisar dokokin kasar nan da ta amince da kudirin biyan mafi karancin albashi na N70k
Tinubu ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta amince da kudurin dokar mafi karancin albashi ya zama dokar da za,a Fara aiki da ita
Bukatun Hakan na kunshe ne a cikin wasikun da aka aike zuwa ga shugabannin majalisun guda biya tsakanin majalisar dattawa data wakilai
Tajudeen Abbas shine kakakin majalisar ya karanta wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Kudirin ya bukaci a tsara mafi karancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi kwanan nan da kungiyoyin kwadago.
Idan za,a iya tunawa jaridar inda ranka ta rawaito cewa Hakan na zuwa ne daidai lokacin da aka cimma matsaya a ysakanin kungiyoyin kwadago ta TUC da NLC da Kuma gwamnatin tarayya
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
