News
GWAMNAN JIGAWA YA SHAWARCI AL,UMMUR NIGERIA KADA SUYI ZANGA- ZANGA SU CIGABA DA ADDU,OI DOMIN NEMAN MAFIA
DAG YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Jigawa alhaji Umar Namadi ya ce zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar a ranar 1 ga watan Agusta, ba ita ce mafita ga kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu ba.
Gwamnan ya bayyana hakanne a wani taro da aka yi da kungiyoyi 27 da ya gudana ranar litinin a birnin Dutse ta jihar jigawa
Namadi yace tabbas Nijeriya na fama da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tabbas ga Kuma matsalolin rashin tsaro
Amma, zanga-zangar ba ita ce mafita ba. Akwai hanyoyi da dama da mutane za su iya bayyana kokensu, mutane suna da ‘yancin nuna korafe-korafensu ta hanyar zanga-zangar karkashin mulkin dimokradiyya, amma wannan ba ita ce hanya mafi inganci don magance matsalolin ba.
Yace zanga-zanga kadai ba za ta samar da mafita ba, jama’a su koma ga Allah, su tuba, su nemi gafara da sa hannun Ubangiji kan kalubalen da kasa ke ciki.
Namadi ya ce gwamnati ta yi iyakacin kokarinta ta fuskar samar da kayan abinci da sauran kayayyaki da suka hada da raba kudade domin rage wahalhalun da jama’a suke fuskanta a dukkan matakan gwamnati.
Gwamnan ya kuma tunatar da jama’a cewa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta amince da shigo da kayan abinci cikin kasar na tsawon watanni biyar ba tare da harajin shigo da kaya daga kasashen waje ba.
Namadi ya shawarci ‘yan Nijeriya da su yarda da wahalhalu a matsayin jarabawa daga Allah, ya kara da cewa kowane musulmi yasan kaddara ko mai kyau ko mara kyau don haka al’umma su cigaba da addu’ar samun sauki ga kasa.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
