Connect with us

News

 Hukumar DSS Ta Bankado Wata Kungiyar Fataucin Yara, Ta Kama Wasu Mutane Biyu A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar ‘yan sandan farin kaya  ta (DSS) ta bankado wata kungiyar fataucin yara tare da kama wata mata ‘yar shekara 17  da ake daukar nauyinta tare da gano wata yarinya ‘yar shekara 4 mai suna Aisha da aka sace daga Nguru a jihar Yobe.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa ofishin hukumar DSS na Kano ne ya bayyana hakan  a ranar Talata,

Haka zalika ya kara da cewa Jami’an Hisbah na Jihar Kano sun mika wa wata yarinya ‘yar shekara 4 mai suna A’isha da aka yi garkuwa da ita daga Nguru wadda wata mata ‘yar shekara 17 da aka  sakaya sunanta ta kawo ta  Kano bayan sun yi garkuwa da ta .

Hukumar DSS ta bayyana cewa bayan karbar Aisha ‘yar shekara 4 da aka sace tare da wanda ta sace ta, sun gano mutumin da ke safarar kananan yara daga Jihohin Makwafta inda ake sayar da su a Kudancin kasar nan.

“Mun kama babban mai safarar kananan yara daga jihohin makwabta zuwa Kano tare da sayar da su a Kudancin kasar nan.

Advertisement

Hukumar DSS ta ce bayan yi wa matar mai shekaru 17 tambayoyi, ta tabbatar musu da cewa mutumin da ta san yana sayar da goro ya shigar da ita cikin lamarin  garkuwa da Aisha ‘yar shekara 4, kuma ya yi mata alkawarin cewa babu abin da zai same ta.

Shugaban  masu garkuwa da yaran, ya  tabbatar da cewa sace Aisha ‘yar shekara 4, shi ne mugun hali na uku da ya aikata daga Nguru.

“Na yi sa’a bayan da na yi amfani da wannan matar ta dauko min Aisha ta  kawo ta Kano inda a kullum nake tattara yaran da aka sace in biya wadanda suka sace ni kuma zan siyar da su ga abokan aikina,” in ji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending