News
Hukumar EFCC Ta Kama Ma’aikacin Banki Da Wasu Mutane 3 Da Suke Damfari Makudan Kudade A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Kano sun kama ma’aikacin bankin da wasu mutane uku masu suna Ismail Ibrahim Ilu, Lamido Bala da Abba Mohammed.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a hanyar Unity Road, Kantin Kwari, Kano, biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan wasu mutane da ake zargi da satar makudan kudade a cikin tsabar kudi.
Hukumar DSS Ta Bankado Wata Kungiyar Fataucin Yara, Ta Kama Wasu Mutane Biyu A Kano
Sanarwar ta ce, wadanda ake zargin sun kware wajen karbar kudaden Naira daga bankuna daban-daban da nufin cire wasu ‘yan kudade daga kowanne su ajiye su a asusun ajiyarsu na banki a wani banki inda mai laifin nasu zai karbi kudin a matsayin asali.
“Wadanda ake zargin sun aikata wannan aika-aika ne ta hanyar zuwa bankunan su suna neman wata lamba (a cikin Naira N200) tare da cire wasu ‘yan takardu a cikin kowane daure.
Daga nan sai su kai wa abokin aikinsu a bankin wanda zai karbo kudin ya shigar da su kamar yadda aka cika masu ba tare da kirga su a kan yarjejeniyar cewa za su ba shi kasonsa na kudaden da suka cire ba,” in ji Oyewale.
Sanarwar ta ce, an kwato jimillar kudi Naira miliyan bakwai da dubu dari biyar (Miliyan Bakwai, Naira Dubu Dari Biyar) daga hannun wadanda ake zargin a lokacin da aka kama su.
EFCC ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
