News
Hukumar DSS Ta Bayar Da Belin Shugaban Kungiyar Kwadago Joe Ajaero
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bada belin shugaban kungiyar kwadago na Najeriya, NLC, Joe Ajaero bayan Kama shi da tayi a safiyar litinin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani mai rajin kawo cigaban jama’a kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a daren Litinin.
Ambaliyar Ruwa: Zulum Ya Rufe Ɗauƙacin Makarantun Firamare Da Ke Jihar Nan Take
An kama Ajaero a safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, a akan hanyar sa ta zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance.
Ajaero dai zai halarci taron kungiyar ‘yan kwadago da za a yi a Landan, wanda za a fara a litinin dinnan.
Advertisements
