News
Jami’an Tsaro Sun Gayyaci Shugaban NLC Kan Zargin Tallafa Wa Ta’addanci
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rundunar ƴan sanda ta gayyaci shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero kan zarginsa da hannu a cikin ɗaukar nauyin ta’addanci da wasu laifukan da suka shafi sata a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda, IRT ya fitar, rundunar ta umarci Ajaero ya hallara a ofishin IRT a ranar Talata 20 ga watan Agusta.
Kungiyar ASUU Ta Fitar Da Sanarwar Tafiya Yajin Aiki Nan Da Kwanaki 21
Sanarwar ta ce, “wannan ofishin na bincike kan laifukan makircin fashi, ɗaukar nauyin ta’addanci, zamba cikin aminci, maƙarƙashiya da sata ta yanar gizo waɗanda aka ambaci sunanka.”
Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa, za a kama shi matuƙar ya ƙi amsa wa kiran da aka masa.
Advertisements
