Connect with us

News

Rundunar Ƴan Sandan Ta Ceto Yaro Dan Shekara 4 Da Wasu Mutane Uku Suka Yi Garkuwa Da Shi A Kano

Published

on

Rundunar Ƴan Sandan Ta Ceto Yaro Dan Shekara 4 Da Wasu Mutane Uku Suka Yi Garkuwa Da Shi A Kano

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da ceto Muhammad Nasir yaro dan shekara 4 da wasu mutane uku suka yi garkuwa da shi a unguwar Sharada Quarters.

Advertisement

Kakakin rundunar ƴan sanda jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai , ya ce an yi garkuwa da yaron ne inda aka gudu da shi garin Gwarzo, aka kuma biya kudin fansa Naira miliyan 10.

Hukumar DSS Ta Bayar Da Belin Shugaban Kungiyar Kwadago Joe Ajaero

A cewar Kiyawa, bayan tattaunawa an biya naira 300,000, da yarjejeniyar za a ciki sauran kuɗin,inda rundunar ƴan sandan ta yi nasarar kama mutane uku: Hisbullahi Salisu mai shekaru 30, Hassan Ali Rabiu mai shekaru 28 da kuma Hassan Aliyu mai shekaru 22 dukkansu ƴan Kano.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa babban wanda ake zargin, Hisbullahi Salisu, wanda ya kasance dan uwa ne ga yaron da aka sace,ya amsa laifin hada baki da sauran wadanda ake zargin wajen yin garkuwa da wannan yaro. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa an yi nasarar kubutar da yaron har an mika shi ga iyayen sa.

Haka kuma Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yabawa tawagar da suka sa ido game da irin matakin gaggawa da suka dauka wanda hakan ya kai ga nasarar ceto wannan yaro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending