Connect with us

News

Tsadar ƙwai da nama sun sanya al’umma neman mafita da roƙon gwamnati

Published

on

Tsadar ƙwai da nama sun sanya al’umma neman mafita da roƙon gwamnati

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Al’umma na cigaba da kokawa game da tashin gwauron zabi da farashin ƙwai da nama ke yi babu ƙauƙautawa.

Advertisement

Mafi yawa daga cikin mutanen da suka yi irin wannan koke sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a Abuja, cewa tsadar farashin na ya fara sa su kasa siya wa ‘ya’yansu ƙwai (musamman yara) da suke da buƙatar sinadarin furotin.

Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Yi Tafiya, Yayin Da Rikici Ke Ƙara Tsamari A Jami’yyar NNPP A Kano

Sun kuma miƙa kokensu ga gwamnatin domin taimaka musu wajen kawo ƙarshen tsadar farashin domin su iya samun zarafin siya.

Advertisement

Wata mata mai suna Christiana Agede, ta ce ana sayar da kilo ɗaya na naman sa a baya Naira 4500 zuwa 5000, amma yanzu ya dawo Naira 6500 zuwa 7000.

Agede ta ce ba ta iya zuwa ta siya yanzu saboda ba ta da isasshen kuɗi kuma ƙwai ma da sukan siya, yanzu ya fi ƙarfin iyalinta saboda tsada.

Advertisement

“A yanzu muna siyan tantaƙwashi ne a maimakon nama a gidajenmu, domin idan ka siyi na 1500 yana da yawa ga kuma sinadarai masu gina jiki,” matar ta bayyana.

Ta ce ‘ya’yanta ba sa son tantaƙwashin, amma a tilas ta nuna musu muhimmancinsa da irin alfanunsa.

Advertisement

Ita ma Henrietta Daniel, da ke da ‘ya’ya, ta ce dole ta sa ta ta cire batun ƙwai daga cikin lissafin abin da za su riƙa ci saboda tsadar da suka yi.

“A gaskiya akwai lokacin da ‘ya’yana kan ci abinci ba tare da wani sinadarin furotin ba, duk da na san hakan na da illa ga girmansu. Ya kamata gwamnati ta taimaka ta samo mana mafita game da wannan tsada,” matar ta faɗa.

Advertisement

Misis Adaeze Asiji, wacce ita ma ke siyan kaji, ta ce farashin kaji ya yi tashin gwauron zabi, inda a baya ta ce ana sai da kilon kaza a kan Naira 3500 zuwa 4000, amma a yanzu ana sayar da kazar ne a kan 5000 zuwa 6500.

Misis Elizabeth Adodi, ma’aikaciyar gwamnati ce, ita ma ta nuna damuwarta game da ƙaruwar farashin nama, inda ta roƙi gwamnati kan ta taimaka wajen ganin an rage farashin abinci da na nama a ƙasar nan.

Advertisement

A yayin da yake bayani game da dalilan da suka jawo tsadar nama, wani mahauci da ke kasuwar Mararraba, Everistus Nnamani, ya ce ƙarin kuɗin sufuri ne ya jawo ƙaruwar farashin.

Ya ce suna siyan ƙaton sa a kan Naira 8000,000 a baya amma yanzu ya kai miliyan 1 zuwa miliyan 1 da rabi.

Advertisement

Ƙaramin sa kuwa da ana sayensa ne a kan Naira 400,000 ko 500,000 amma yanzu ya dawo Naira 600,000 zuwa 700,,000.

Kuma duk ya alƙanta tashin farashin da tsadar man fetur da dizal da kuma matsalar tsaro.

Advertisement

Ya ce yawan tashin farashin dabbobi na shafar kasuwancinsa, domin a da yana iya siyan shanu 6 ya yanka su kuma ya sayar.

Amma yanzu a cewarsa da ƙyar yake iya sayen sa 1 kuma duk ribar tasa ma na shigewa ne wajen sake siyan wani sa ɗin.

Advertisement

A wani dalili da ke ƙara tashin farashin shanu a kasuwa shi ne batun matsalar satar mutane, domin yanzu masu satar mutane sun fi son su saci motar shanu a maimakon mutane tare da sayar da su.

Shi kuwa, mista Kelechi Odo, wani mahauci, ya ce ba komai ne ke haifar da tsadar nama ba facce taɓarɓarewar musayar kuɗi, domin sukan sayi dabbobinsu yawanci daga ƙasashen Nijar da Kamaru ne.

Advertisement

Ya ce farashin ƙaramar dabba a baya Naira 15,000 zuwa 18,000, amma yanzu Naira 25,000 zuwa N28,000 ake sayar musu

Sannan dabba matsakaiciya ana sayar da ita da a kan Naira 27,000 zuwa Naira 28,000 idan aka yi la’akari da farashin da ake sayarwa a baya na Naira 20,000 zuwa N22,000.

Advertisement

Su kuwa manyan dabbobi (akuyoyi) ana sayar da su a kan Naira 32,000 zuwa Naira 35,000 saɓanin Naira 28,000 da ake sayarwa a baya.

Shi ma Alhaji Yusuf Ali, wanda dilan sayar da raguna ne a kasuwar dabbobi ta Kugbo, ya ce a yanzu ana sai da rago ne tsakanin Naira 50,000 zuwa Naira 150,000 duk da hakan ya danganta da girmanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending