Uncategorized
Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Yi Tafiya, Yayin Da Rikici Ke Ƙara Tsamari A Jami’yyar NNPP A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi tafiya zuwa Abuja, yayin da rikici ke ƙara tsamari a jami’yyar NNPP a jihar.
A ranar Litinin, gwamnan Jihar ya yi sasanci tsakanin Sakataren Gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi, da wasu wakilan mazaɓarsa da suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda abubuwa ke tafiya.
Kusan Duka Ƴan Majalisun Najeriya Ƴan Ƙwaya Ne, Sannan Suna Fataucin Muggan Ƙwayoyi —Sanata Sumaila
Duk da sasancin gwamnan, jam’iyyar ta dakatar da Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol, bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar.
AMINIYA ta ruwaito cewa Gwamnan ya yi jiran kusan sa’o’i biyu a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, kafin daga bisani ya tashi zuwa Abuja.
A lokacin da gwamnan ya yi tafiya, jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na ganawa jiga-jigan jam’iyyar jihar.
Ko da aka tambayi Kwankwaso kan rikicin NNPP, ya ƙi yin tsokaci, inda ya ce shugabannin jam’iyyar sun ɗauki matakin da ya dace.
A baya-bayan nan dai wasu sun nuna damuwa kan irin ikon da Kwankwaso ke da shi a siyasar gwamnatin Kano, wanda suke ganin hakan yana hana Gwamna Yusuf gudanar da ayyukasa yadda ya kamata.
Hakan ne ya sa wasu ƙungiyoyi fara kiran da “Abba Tsaya da Kafarka”, a wani yunkuri na raba Gwamnan jihar da Kwankwaso.
Sai dai wannan kiranye-kiranye da ake yi wanda aka alaƙanta su da Sakataren Gwamnatin jihar, amma ya musanta zargin.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
