News
Shugaban Tinubu Ya Gana Da Firai Ministan India Narendra Modi A Fadarsa Dake Abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana da Firai Ministan India Narendra Modi a fadarsa dake Villa babbban birnin Tarayya Abuja a yau lahadi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito a jiya Asabar ce Firai Ministan India Narendra Modi ya iso Nageriya a ziyarar da ya kawo domin kara kulla alaka mai karfi a tsakanin Kasashen biyu.
Haka zalika Shugaban Tinubu Ya jinjinawa Narendra Modi inda ya bashi , lambar girmamawa ta Najeriya mafi alfarma ta GCON. Inda shugaban ya ce Hakan alama ce ta yabo da jajircewar Najeriya.
A kawancen da Najeriya da kasar Indiya suka kulla Kasashen sun jaddada aniyar gina kwakkwarar alaka, inda suka sha alwashin karfafa dangantaka a muhimman fannoni irinsu bunkasa tattalin arziki da tsaro da kiwon lafiya da kuma samun wadatar abinci.
A yayin tattaunawar tasu, shugabannin 2 sun amince da samun karin hadin gwiwa a fannin yaki da ta’addanci da tsaron teku da kuma musayar bayanan sirri.
Ratotannin na nuni da cewa wannnan shine Karo na farko da Firai ministan India ya kawo ziyarar Najeriya tun bayan , ziyarar da karamin firai minista Dr Manmohan Singh ya kawo a shekara ta 2007, lokacin da kasashen biyu suka kulla kawance mai inganci.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
