News
Za’ A Samu Saukin Farashin Litar Man Fetur Zuwa Ranar Litinin – IPMAN
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta IPMAN, ta ce farashin man fetur zai ragu zuwa N935 a kowace lita a ranar Litinin duba da sabon farashin da matatar man Dangote ta fitar.
IPMAN ta ce sabon ragin farashin ya biyo bayan rage farashin man fetur da matatar Dangote ta yi da kuma tsarin bai daya, wanda zai baiwa ‘yan kasuwa damar siyar dashi akan Naira 935 a gidajen mai masu zaman kansu a fadin Kasa.
shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Mai Gandi Girima shi’ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN a Abuja, babban birnin Tarayya inda ya bayyana Sabon farashin matatar Dangote a matsayin cigaba
Rahotanni sun tabbatar da matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur da kashi 7.27 daga naira 970 zuwa naira 899.50 kan kowacce lita tare da da baiwa kananan ‘yan kasuwa bashi.
Matatar man Dangote tace ta tsara rage farashin ne domin rage tsadar sufuri a lokutan bukukuwan Sabuwar Shekarar da kirsimeti , Wanda aka Fara siyar dashi Kan Naira 935 a Jihar Legas, kuma za a fara bada shi a farashin haka a fadin Jihohin Kasar zuwa ranar Litinin.
Baya ga haka matatar Dangote ta sake kawo wani sabon tsari na baiwa kana nan ‘yan kasuwa damar siyan Mai akan farashin na Naira 899. 50 don siyar dashi a gidanen mansu.
Shugaban IPMAN ya ce a baya suna lodin Man Kan Naira N970 kan kowace lita a matatar Dangote, amma bisa tsari da alkawarin da Dangote ya yi, cewa zuwa ranar Litinin farashin mai zai ragu zuwa N935
(NAN)
