Connect with us

News

Za’ A Samu Saukin Farashin Litar Man Fetur Zuwa Ranar Litinin – IPMAN

Published

on

 

 

Advertisement

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta IPMAN, ta ce farashin man fetur zai ragu zuwa N935 a kowace lita a ranar Litinin duba da sabon farashin da matatar man Dangote ta fitar.

 

Advertisement

IPMAN ta ce sabon ragin farashin ya biyo bayan rage farashin man fetur da matatar Dangote ta yi da kuma tsarin bai daya, wanda zai baiwa ‘yan kasuwa damar siyar dashi akan Naira 935 a gidajen mai masu zaman kansu a fadin Kasa.

 

Advertisement

shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Mai Gandi Girima shi’ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN  a Abuja, babban birnin Tarayya inda ya bayyana Sabon  farashin matatar Dangote a matsayin cigaba

 

Advertisement

 

Rahotanni  sun tabbatar da  matatar man Dangote ta  sanar da rage farashin man fetur da kashi 7.27 daga naira 970 zuwa naira 899.50 kan kowacce lita tare da  da baiwa  kananan ‘yan kasuwa bashi.

Advertisement

 

 

Advertisement

Matatar man Dangote tace ta  tsara rage farashin ne domin rage tsadar sufuri a lokutan bukukuwan Sabuwar Shekarar da kirsimeti , Wanda aka Fara siyar dashi Kan Naira 935 a Jihar  Legas, kuma za a fara bada shi a farashin haka a fadin Jihohin Kasar zuwa ranar Litinin.

 

Advertisement

Baya ga haka matatar Dangote ta sake kawo wani sabon tsari na baiwa kana nan  ‘yan kasuwa damar siyan Mai akan  farashin na Naira 899. 50 don siyar dashi a gidanen mansu.

 

Advertisement

Shugaban IPMAN ya ce a baya suna lodin Man  Kan Naira N970 kan kowace lita a matatar Dangote, amma bisa tsari da alkawarin da Dangote ya yi, cewa zuwa ranar Litinin farashin mai zai ragu zuwa N935

 

Advertisement

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending