News
Malan Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo “Ya Zama Cikakken Farfesa A Sashen Nazarin Hadisi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jami’ar Bayero (BUK ) ta naɗa Malan Muhammad Sani Umar R/Lemo daga Mataimakin Farfesa zuwa cikakken Farfesa.
Jami’ar ta ce tayi farin ciki da murnar zamowar malamin cikakken Farfesa daga mukamin karamin Farfèsa.
Jaridar Daily Reality ta rawaito Malamin ya zamo Farfesa a Sashen Nazarin Hadisi wanda hukumar gudanarwar Jami’ar ta ce ya kware kan zantuka na hadisan Annabi Muhammad (SAW).
Sanarwar ta cigaba da cewa wannan nadin da akayiwa Malamin ya biyo bayan chanchnatarsa da aiki tuƙuru tsawan shekaru masu yawa da aiki a duniyar ilimi da ilimin Islama.
Mutane da dama ciki harda abokakan aikinsa abokan Ilimi da dalibansa ne suka tayashi murna tare da yimasa addu’o’in samun nasara da kuma karin albarka a sabon matsayin daya zama.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
