News
An Zargi Yan KAROTA Da Zambatar Direbobin Adaidaita Sahu Kudin Tracker Sama Da Miliyan 560 —Bincike
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A shekarar 2020 hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA karkashin jagorancin tsohon Manajan Daraktanta, Baffa Babba Dan’agundi ta kaddamar da wata manufa da ta yi alkawarin kawo sauyi ga harkar zirga-zirgar Adaidaita Sahu a Kano.
Shirin ya umarci dukkan masu gudanar da aikin Adaidaita Sahu, su biya Naira 8,000 kowannensu domin masu GPS da aka tsara domin inganta tsaro, lura da motsinsu, da kuma dakile miyagun laifuka.
Gwamnan Kano Ya Sanya Hannu Kan Kasafin Kuɗin Shakarar 2025 Na Naira Biliyan 719
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa maimakon cika wadannan alkawurran, KAROTA ba ta ba wa masu aiki komai ba illa sitika, wadanda da yawa suka bayyana a matsayin abubuwa marasa amfani da ba za su iya bin diddigin motsi ko inganta tsaro ba
Inda ake zargin sun damfari masu sana’ar Adaidaita Sahu guda 70,000 da suka haura Naira miliyan 560.
Kasuwancin Adaidaita Sahu, wanda ya samu bunkasuwa bayan hana zirga-zirgar baburan Achaba a shekarar 2005, ta samar da hanyar rayuwa ga mazauna Kano sama da 100,000 da suka hada da masu haya, masu gida, da kanikanci. Ga waɗannan ma’aikatan, alƙawarin tsaro ya kasance mai yuwuwa.
Yawancin mahayan Adaidaita Sahu sun bi umarnin, suna ganin masu bin diddigin GPS za su kare rayuwarsu, sai kawai suka gano an yaudare su.
Rahotanni na nuni da cewa ga dukkan alamu wannan na daya daga cikin manyan zamba da ake zargin Kano, inda suka damfari masu sana’ar Adaidaita Sahu miliyoyin naira ta hanyar wani shiri na bogi wanda cikin gaggawa ya zama mafarkin karya alkawari da kuma tambayoyin da ba a amsa ba.
