Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Da Ke Shirin Zuwa Australia 

Published

on

Nigeria Australia

DAGA AMINA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da ke shirin tafiya zuwa kasar Australia da su sani cewa akwai biranen kasar dake fama da tabarbarewar tsaro.

Advertisement

Cikin sanarwar da mukaddashin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Mr. Kimiebi Imomotimi Ebienfa yace “ Bisa lura da rahotannin nuna wariya, cin zarafi da zagin baki ‘yan kasashen waje, kyamar musulmai ya zama wajibi mu sanar tare da nunawa dukkan masu shirin tafiya koma ‘yan Najeriya dake zaune a kasar Australia hatsari da zasu iya fuskanta na yiwuwar barkewar rikici a wasu birane.”

An Zargi Yan KAROTA Da Zambatar Direbobin Adaidaita Sahu Kudin Tracker Sama Da Miliyan 560 —Bincike

A farkon watan Disambar shekarar 2024 dai an sami hare-haren kin Musulmai da ma Yahudawa a wani kauye da ke gefen birnin Sydney.

Advertisement

Wannan gargadi na zuwa ne sa’o’i bayan da kasar Australia ta yi wa ‘yan kasarta gargadi kan su guji yinkurin zuwa Najeriya saboda matsalar tsaro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending