Connect with us

News

Majalisar Dokokin Kano Ta Bukaci Sake Duba Dokar Amfani da Ƙasa

Published

on

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Zaben Kananan Hukumomin Da Aka Shirya Yi

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Majalisar dokokin Jihar Kano ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta duba yiwuwar yin garambawul ko sake nazari kan dokar amfani da ƙasa (Land Use Act), duba da yadda tattalin arzikin ƙasa ke fuskantar sauye-sauye.

Advertisement

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, kuma shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ‘Yan-Gurasa, ne ya gabatar da kudirin gaggawa a zaman majalisar na yau Litinin.

Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Ƙarar Fubara Kan Shugabancin Majalisar Dokokin Ribas

Dokar amfani da ƙasa ita ce ke tsara yadda ake rarraba, mallaka, da amfani da ƙasa a Najeriya. Dokar ta bai wa gwamnati ikon mallakar duk wata ƙasa, tare da bai wa gwamnoni ikon bayar da izini ga mutanen da za su yi amfani da ita.

Advertisement

Majalisar ta bayyana cewa, duba da yadda tattalin arzikin ƙasa ke canzawa, akwai buƙatar yin bitar wannan doka domin tabbatar da cewa tana amfanar al’umma da ci gaban jihar.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending