Connect with us

News

Manoma Cikin Fargaba Yayin Da Gonakinsu Ke Bushewa Sakamakon Kafewar Dam Din ‘Yan Ganau A Kano

Published

on

Manoma cikin fargaba yayin da Gonakin su ke bushewa saboda kafewar Dam din 'Yan Ganau a Tsanyawa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Daruruwan manoma ne ke cikin damuwa bayan da suka zuba milyoyin naira domin noman rani a kewayen dam din ‘Yan Ganau da ke karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano, amma yanzu haka amfanin gonakinsu na fuskantar barazanar bushewa saboda kafewar dam din.

Advertisement

Manoman sun bayyana cewa ko rijiyoyin da suke tona domin samun ruwa sun yi nisa, kuma ba su da ikon saka riyojin burtsatse saboda matsin tattalin arziki da suke fama da shi.

Idan Kana Azumi Kada Ka Rasa Waɗannan Abubuwa 11  – Sheikh Daurawa

Daya daga cikin manoman da ya zanta da AREWA RADIO mai suna Rahamatullahi Abdussalam, ya ce suna kallo amfanin gonakinsu kamar masara, tumatir da sauran kayan lambu na milyoyin naira na bushewa, yayin da ba su da ikon kaiwa ga ruwan da ke karkashin kasa.

Advertisement

Manoman sun bayyana cewa a shekarar da ta gabata Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya tura ayyukan gyara zuwa dam din, amma daga karshe aikin bai gudana yadda ya kamata ba.

A halin yanzu, manoman sun yi kira ga shugabannin karamar hukumar Tsanyawa, dan majalisar wakilai na Tsanyawa da Ghari, Sanata Barau Jibrin, da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da su gaggauta kai dauki domin ceton gonakinsu daga bushewa.

Advertisement

Sun bayyana cewa idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, miliyoyin naira da suka saka a cikin noman ranin na iya salwanta, lamarin da ka iya haifar da karancin abinci da tabarbarewar tattalin arziki a yankin.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending