News
Gwamnatin Tarayya a Ta Maka MultiChoice Ta Kotu Kan Ƙarin Kuɗin DSTV Da GOtv
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar kula da ayyukan kamfanoni da walwalar kwastomomi ta Najeriya (FCCPC) ta maka kamfanin MultiChoice Nigeria, mallakin layukan DSTV da GOtv, a kotu kan zargin karya dokokin kwastomomi.
Sanarwar da hukumar ta fitar a yau Laraba ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan da MultiChoice ta ƙi janye ƙarin kuɗin sabis da ta sanar tun ranar 24 ga watan Fabrairu duk da umarnin da aka ba ta.
Kamfanin ya fara aiwatar da sabon tsarin kuɗin ne daga ranar 1 ga watan Maris, matakin da ya janyo cece-kuce da ƙorafe-ƙorafe daga ‘yan Najeriya.
FCCPC ta ce tana ci gaba da bincike kan halascin ƙarin kuɗin, tare da bukatar kamfanin ya dakatar da aiwatar da sabon farashin har sai an kammala binciken.
Sai dai a cewar hukumar, MultiChoice ta ƙi bin wannan umarni, abin da ya sa aka garzaya kotu don neman hukunci.
