Connect with us

News

Allah Ya Yi Wa Sakataren NRO, Injiniya Abdulkadir Gude Rasuwa

Published

on

IMG 20250509 WA0003
Advertisements
ads

Allah Ya yi wa Sakataren Kungiyar Northern Reform Organization (NRO), Injiniya Abdulkadir Yusuf Gude, rasuwa.

Injiniya Gude ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekara 65 a duniya, bayan fama da doguwar jinya.

Matsalar Wuta: Najeriya Na Da Arziki, Amma Jama’a Na Rayuwa A Duhu

Marigayin yana daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar NRO, wadda aka kirkira domin tallafa wa yankin Arewa wajen fuskantar matsalolin da ke damunta tare da kawo sauyi mai amfani.

An san Injiniya Gude da kishin kasa da sadaukarwa wajen aiki tukuru don ganin Arewa ta ci gaba.

Ya shafe shekaru yana aiki a Hukumar Albarkatun Ruwa da Ayyukan ta Kano wato Kano water resources and engineering construction agency (WRECA)  da kuma a Kamfanin Aluminium Smelter Company da wasu cibiyoyi da dama.

Daya daga cikin aminansa, Mahmoud Adnan Audi, ya tabbatar da rasuwar Injiniya Gude, inda ya ce za a gudanar da jana’izarsa bayan sallar Juma’a da misalin karfe 2:30 na rana a tsohuwar harabar Jami’ar Bayero da ke Kano.

Advertisement

Muna  rokon Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending